(ABNA24.com) A Amurka, batun cin zarafi da kisan bakaken fata na kara muni, a kasar inda a baya bayan nan wani bakar fata ya rasa ransa a hannun wani jam’in dan sanda.
Hoton bidiyon da aka wallafa a shafukan sada zumunta ya kara nuna yadda bakaken fata ke fuskantar muzguna daga jami’an ‘yan sandan na Amurka.
Hoton ya nuna wani dan sanda ya danne wuyan bakar fatan mai suna George Floyd, da gwiwa, har ya mutu.
Tuni gwamnatin jihar Minneapolis ta sallami wasu ‘yan sanda hudu da aka samu da hannu a kamen bakar fata.
A shafinsa na Twitter, Magajin garin Minneapolis Jacob Frey ya rubuta cewa sallamar jami’an ‘yan sandan shi ne abin da ya dace.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ‘yan sanda Amurka ke kashe bakaken fata, bisa wata hujja marar tushe.
/129
28 Mayu 2020 - 05:07
Lambar labari: 1040851
A Amurka, batun cin zarafi da kisan bakaken fata na kara muni, a kasar inda a baya bayan nan wani bakar fata ya rasa ransa a hannun wani jam’in dan sanda.